Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci a gudanar da bincike kan kisan fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da daren Laraba, Kwankwaso ya bayyana kisan a matsayin “mummunan hari”, inda ya bukaci gwamnatin Kano ta gaggauta kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban shari’a.
Kwankwaso ya ce idan gwamnatin yanzu ta gaza daukar matakin da ya dace, gwamnatin NDC za ta sake bude batun tare da gudanar da sabon bincike idan aka zabe ta a 2027, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jagoran adawar ya kuma yi kira ga hukumomin jihar da na tarayya da su tabbatar da kare masu sukar gwamnati da masu ra’ayoyin adawa, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da ’yancin fadin albarkacin baki.
An samu gawar Dan Shagamu, mai shekaru 54 kuma mahaifi ga ’ya’ya shida a gidansa da ke Gaida, karamar hukumar Kumbotso, lamarin da ya janyo Allah-wadai a fadin jihar.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ita ma ta yi Allah-wadai da kisan, inda ta yi gargadin karuwar barazanar da ake fuskanta kan ’yan jarida da masu sharhi a gabanin zaben 2027.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan, yayin da take ci gaba da bincike.
Rundunar ta ce da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Kwankwaso
