Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, sun ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa sansanonin siyasarsu gabannin babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dukkan sansanonin ‘yan takarar uku na dogaro ne da tsare-tsaren jam’iyyunsu, ƙawancen siyasa, da ƙungiyoyin magoya baya domin samun nasara a jihohi da dama fiye da waɗanda suka lashe a zaɓen 2023.
A zaɓen na 2027 mai zuwa, Shugaba Tinubu zai fafata a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Atiku Abubakar zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, yayin da Peter Obi zai fafata a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
A zaɓen 2023 da ya gabata, Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726 inda ya lashe jihohi 12 da suka haɗa da Ekiti, Ogun, Oyo, Kwara, Ondo, Jigawa, Benue, Niger, Kogi, Zamfara, Rivers, da Borno. Shi kuwa Atiku ya samu ƙuri’u 6,984,520 inda ya lashe jihohi 12 da suka haɗa da Osun, Yobe, Katsina, Adamawa, Taraba, Kaduna, Bayelsa, Sokoto, Akwa Ibom, Bauchi, Kebbi, da Gombe. A nasa ɓangaren, Peter Obi ya samu ƙuri’u 6,101,533 inda ya lashe jihohi 11 tare da birnin tarayya Abuja (FCT).
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa, jam’iyyar APC ta bayyana cewa tana da tsari mai ƙarfi fiye da na shekarar 2023, inda wani babban jigo a jam’iyyar ya bayyana cewa burinsu shi ne su lashe aƙalla jihohi 20, ciki har da Lagos, Rivers, Kano, da Kaduna, musamman ganin yadda gwamnonin da suka fito daga jam’iyyun adawa suka sauya sheƙa zuwa APC.
Shugaban ƙungiyar All Progressives Congress Forum ta shiyyar Arewa ta Tsakiya, Alhaji Saleh Zazzaga, ya bayyana cewa a yanzu APC na da gwamnoni kusan 31 idan aka kwatanta da 22 da take da su a 2023, yana mai jaddada cewa Shugaba Tinubu zai share dukkan jihohin Kudu maso Yamma da kuma ƙarin jihohi kamar Plateau da Nasarawa.
A ɓangaren jam’iyyar ADC, tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya tsara dabarun da za su ba shi damar riƙe jihohinsa tare da lashe ƙarin jihohi a 2027.
Nwosu ya ce binciken jin ra’ayin jama’a da suka gudanar ya nuna cewa Atiku zai samu kaso 63 cikin 100 na ƙuri’un ƙasar, kuma zai samu aƙalla kaso 25 na ƙuri’u a jihohi 28, yana mai jaddada cewa fiye da kaso 80 na mambobin PDP da kaso 50 na Labour Party sun koma ADC.
A nasa ɓangaren, Peter Obi na dogaro ne da karɓuwar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin faɗaɗa tasirinsa a Arewacin ƙasar. Babban mai gudanarwa na ƙungiyar Obidient Movement ta ƙasa, Yinusa Tanko, ya bayyana cewa haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso ta ƙarfafa jam’iyyar NDC sosai, inda ya bayyana cewa suna da ‘yan takara masu ƙarfi a jihohi irin su Kano da Zamfara, kuma suna da ƙwarin gwiwar sake lashe jihar Lagos sakamakon matsin tattalin arziki da jama’a ke ciki.
