DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiOluremi Tinubu ta buƙaci ’yan Nijeriya su rage ɓarnar abinci

Oluremi Tinubu ta buƙaci ’yan Nijeriya su rage ɓarnar abinci

Uwargidan shugaban ƙasar Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan ƙasa da su rage ɓarnatar da abinci tare da rungumar dabarun da za su kare muhalli daga lalacewa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sanata Tinubu ta yi wannan kiran ne a cikin saƙon taya murnar ranar tsaftace muhalli ta duniya ta shekarar 2026 (World Cleanup Day) da aka gudanar a ranar Lahadi, mai taken: “Daga kwanuka masu tsafta zuwa birane masu tsafta.”

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa mayar da hankali kan batun ɓarnatar da abinci a wannan lokaci ya dace sosai, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen duniya ke ci gaba da kawo cikas ga noman abinci da wadata shi ga al’umma.

“Mayar da hankali kan ɓarnatar da abinci a wannan shekara yana da muhimmanci ƙwarai a daidai lokacin da sauyin yanayi, tashe-tashen hankula, da sauran matsalolin duniya ke ci gaba da shafar noman abinci da wadata shi.”

Ta kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su zama masu lissafi da sanin ya-kamata wajen saye, girki, ci, da kuma adana abinci yadda ya dace a gidajensu.

Ta ƙara da cewa, “Ina ƙarfafa iyalai, ‘yan kasuwa, da al’ummomi da su rage ɓarnatar da abinci, su riƙa zubar da shara a inda ya dace, kuma su ɗauki kyakkyawan tsarin da zai kare muhallinmu.”

Daga ƙarshe, uwargidan shugaban ƙasar ta jaddada cewa haɗa hannu da yin aiki tare a tsakanin kowa ne kaɗai zai ba da damar gina al’umma mai tsafta da ingantacciyar lafiya ga al’ummar yanzu da kuma na gaba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata