DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareCNN, MS NOW da Politico sun kai Trump kotu

CNN, MS NOW da Politico sun kai Trump kotu

Kafafen yaɗa labarai na CNN, MS NOW, da Politico sun shigar da gwamnatin Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ƙara a gaban kuliya bayan an hana ‘yan jaridarsu shiga Fadar White House tare da ƙwace katunan shaidar aikinsu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kafafen yaɗa labaran guda uku sun sanar da ɗaukar matakin shari’ar ne a ranar Litinin, inda suka bayyana cewa suna neman a maido musu da damar shiga fadar tare da kare ‘yancinsu da kwaskwarima ta farko ga kundin tsarin mulkin ƙasar (First Amendment) ta tanadar.

Wannan mataki ya biyo bayan shawarar da Trump ya yanke a ranar Juma’a ta dakatar da waɗannan kafafen yaɗa labarai uku daga fadar gwamnatin, inda ya zarge su da yaɗa abin da ya kira “ƙagaggun labarai da ƙarairayi” game da shi, gwamnatinsa, da kuma ƙasar Amurka.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar a ranar Litinin, CNN, MS NOW, da Politico sun ce, “A safiyar yau, mun sanar da gwamnati cewa muna shigar da ƙara a yau domin kare ‘yancinmu na kundin tsarin mulki da kuma kare ƙa’idar da ta tanadi cewa gwamnati ba ita ke da alhakin kayyade abin da ‘yan jarida za su ruwaito ko wallafa ba.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ba tare da wani gargaɗi ko bin tsari ba, Fadar White House ta ƙwace katunan shaidar aikin ‘yan jaridarmu saboda kawai ba ta gamsu da rahotanninmu ba. Barin wannan mataki ba tare da an ƙalubalance shi a kotu ba barazana ce ga ‘yancin ‘yan jarida da kuma haƙƙin al’umma na samun labarai masu zaman kansu ba tare da tsangwamar gwamnati ba.”

A ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, an hana ‘yan jaridar waɗannan kafafen shiga Fadar White House tare da ƙwace katunansu lokacin da suka isa domin gudanar da aiki. Haka kuma, an cire CNN daga aikin da aka tsara za ta jagoranta a ranar Litinin na wakiltar sauran gidajen talabijin wajen ɗaukar hotunan ayyukan White House tare da bin tawagar Trump zuwa New York domin babban taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA).

Shugaba Trump ya kare matakinsa a shafinsa na Truth Social, inda ya bayyana cewa bai kamata kafafen yaɗa labarai su ci gaba da rubuta ƙarya a kansa da gwamnatinsa ba, yana mai cewa ko da yake yana goyon bayan ‘yancin ‘yan jarida, yana son ‘yan jarida masu gaskiya da adalci ne, kuma ba dole ba ne ya bari su shiga cikin fadar gwamnati da ya kira da “gidan jama’a.”

A halin yanzu, ƙarar da waɗannan kafafen yaɗa labarai suka shigar ta mayar da wannan taƙaddama gaban kotun tarayya domin yanke hukunci kan halascin matakin na Fadar White House.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata