Mata masu zaman kansu da sauran mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar ƙanjamau sun shiga cikin damuwa sakamakon ƙarewar sabuwar allurar rigakafin cutar mai aiki na tsawon watanni shida, wato Lenacapavir, a wasu jihohin Nijeriya.
Binciken da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa allurar ta ƙare a cibiyoyin lafiya na jihohin Benue, Kwara, Gombe, da Cross River, ‘yan watanni kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da tsarin bayar da maganin a gwajin farko.
A Jihar Cross River, ma’aikatan lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Calabar da babban asibitin birnin sun bayyana cewa buƙatar allurar ta ƙaru sosai musamman a tsakanin mata masu zaman kansu.
Wata ma’aikaciyar lafiya a sashin kula da cututtuka masu yaɗuwa a Babban Asibitin Calabar ta bayyana cewa mata masu zaman kansu sun fi zaɓar wannan allura saboda tana da sauƙin ɓoyewa kuma ta fi dacewa da yanayin rayuwarsu, maimakon shan ƙwayoyin magungunan kariya (PrEP) a kowace rana. Sai dai ta ce sakamakon ƙarewar allurar, a yanzu haka suna umartar su da su ci gaba da shan kwayoyin maganin na yau da kullum har sai an samu sabon rukunin allurar.
Haka kuma a Jihar Benue, fiye da mutane 2,000 da ba sa ɗauke da cutar suka karɓi allurar tsakanin watan Mayu zuwa yanzu, lamarin da ya sa maganin ya ƙare a cibiyoyin lafiya. A Jihar Kwara ma, sama da allurai 800 da aka tura a farko sun ƙare.
Da yake mayar da martani, jami’in hukumar yaƙi da cutar ƙanjamau ta ƙasa (NACA), Dokta John Tobias, ya bayyana cewa ƙalubalen sufuri da kuma raguwar kuɗaɗen tallafi daga ƙasashen waje irin su asusun Global Fund na daga cikin abubuwan da suka jinkirta kai magungunan zuwa jihohin a kan kari.
Shi kuwa jami’in lafiya a Jihar Legas ya bayyana cewa a can akwai wadataccen maganin, sai dai mutane ba sa fitowa sosai domin karɓa.
