Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana jam’iyyun adawa da ke shirin fafatawa a babban zaɓen 2027 a matsayin “‘yan kallo kawai” a fagen zaɓe, yana mai jaddada cewa jam’iyya mai ci ta riga ta kammala shiri domin samun nasara a dukkan matakai.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a birnin Maiduguri na Jihar Borno, yayin da yake zantawa da manema labarai a ƙarshen taron kwana uku da aka shirya wa mambobin kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC) na jam’iyyar.
A cewar shugaban na APC, jam’iyyar ta kammala muhimman shirye-shiryen tunkarar zaɓe, ciki har da kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe da kwamitocin sulhu. Ya bayyana cewa jam’iyyar na da cikakken kwarin gwiwa kan ‘yan takarar da ta fitar ta hanyar zaɓen fidda gwani, kuma an ɗauki aniyar faɗaɗa yakin neman zabe domin bayyana ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga masu kaɗa ƙuri’a.
Yilwatda ya ce, “Jam’iyyar na da tagomashi, kuma muna da cikakken yaƙinin cewa mun samar da ’yan takara mafi inganci da karɓuwa da za a zaɓa.”
Da yake mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, Yilwatda ya bayyana cewa tsakanin mambobi 6,000 zuwa 7,000 ne suka fafata a faɗin ƙasar, amma shari’o’i kusan 100 ne kawai aka shigar a kotu.
“Cikin mambobi 6,000 zuwa 7,000 da suka shiga zaɓen fidda gwani, muna da ƙararraki kusan 100 a kotu; wannan na nufin ƙasa da ƙararraki 3 a kowace jiha. Hakan na nuna cewa kaso 1 kacal na waɗanda suka shiga zaɓen suka tafi kotu. Kuna ganin jam’iyyata na cikin matsala kuwa? Kaso 1 kacal ne suka tafi kotu. Muna da cikakken kwarin gwiwa cewa jam’iyyarmu za ta lashe zaɓe,” in ji shi.
Shugaban na APC ya kuma bayyana cewa jam’iyyarsa ce ta farko da ta kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe, inda ya zargi sauran jam’iyyun da gazawa wajen yin hakan a kan kari.
“Mu ne muka fi kowa shiri; mun fafata a zaɓuka da dama kuma mun ci. Manyan jam’iyyun adawa da kuke magana a kansu, babu ɗaya daga cikinsu da ta taɓa cin ko da kujerar kansila; a iya sanina, su ’yan kallo ne kawai a wannan zaɓen,” in ji shi.
A wurin taron, kwamitin na NWC ya kuma aike da saƙon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan mutuwar mutum 37 a hannun hukumomi.
