Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sanya takunkumi tare da dakatar da duk wani nau’i na hawan daba da hawan doki a cikin birnin Kano har sai yadda hali ya yi.
Sanarwar da darakta janar na yaɗa labarai na gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026, ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne a ƙarshen wani taron gaggawa na majalisar tsaron jihar da aka gudanar a gidan gwamnati.
Majalisar tsaron jihar ta cimma matsaya kan ɗaukar wannan matakin riga-kafi ne domin kauce wa duk wani rikici, kiyaye doka da oda, da kuma kare asarar rayuka ko dukiyoyin al’umma.
A cewar sanarwar, rahotannin tsaro sun nuna cewa an fara gagarumar shirin tara magoya baya dangane da hawan da aka tsara gudanarwa, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar samun gumurzu da kuma taɓarɓarewar tsaro a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa duba da nauyin da ya rataya a wuyanta a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na kare rayuka da dukiyoyi, majalisar tsaron ta ba da umarnin dakatar da hawan daban da sauran harkokin hawan doki baki ɗaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa an umarci dukkan hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da bin wannan umarni tare da ɗaukar matakin doka a kan duk wanda aka samu yana karya dokar ko kuma aikata abin da zai iya barazana ga zaman lafiya.
Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci dukkan mazauna jihar, masarautu, ‘yan siyasa, magoya baya, da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalinsu tare da bin wannan doka sau da ƙafa, tana mai ba da tabbacin cewa tana ɗaukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
