Masu garkuwa da mutane sun nemi a biya su N950m domin sakin ’yan NYSC 19 da aka yi garkuwa da su yayin da suke tafiya daga Ibadan zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.
Jaridar Punch ta ruwaito an yi garkuwa da ’yan bautar ƙasar ne a ranar Alhamis, bayan da wasu ’yan bindiga suka tare motocin bas guda biyu da suke dauke da su a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha, a Umunoha da ke jihar Imo.
Manajan Daraktan kamfanin Uko Akwa Ibom Motors Nigeria Limited, Isiah Akpan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan wadanda aka sace tare da neman a biya Naira miliyan 50 kan kowane mutum.
Lamarin ya jefa iyalan wadanda abin ya shafa cikin fargaba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike da sintiri domin gano inda aka kai wadanda aka sace.
Jami’an ’ƴan sanda a Imo sun ce an ceto wasu mutane 10, amma ba a tabbatar ko suna cikin ’yan NYSC din da aka sace ba.
Wata mahaifiya mai suna Oladosu ta shaida cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalinta ta wayar ɗiyarta Greatness, inda suka samu damar ganinta tare da wasu ’yan NYSC a wani bidiyo, suna zaune a cikin daji.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Oyo ta yi Allah-wadai da sace ’yan NYSC din, inda Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Dotun Oyelade, ya ce Gwamna Seyi Makinde ya umarci a yi amfani da dukkanin hanyoyin da suka dace wajen ganin an ceto wadanda aka sace lafiya.
Masana tsaro sun ce yawan sace ’yan NYSC na bukatar a sake duba tsarin tura matasa zuwa wuraren da ke fama da matsalar tsaro, tare da ƙarfafa matakan kariya ga masu zuwa sansanonin horaswa.
Sun kuma ce ana bukatar gwamnati da hukumar NYSC su samar da tsare-tsaren sufuri da tsaro na musamman ga ’yan bautar ƙasar a lokutan tafiye-tafiyensu.
