Ƙungiyar da ke shiga tsakani kan harkokin ma’aikatan gwamnati ta ƙasa, JNPSNC, ta ayyana yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga ranar 2 zuwa 4 ga Oktoba 2026.
Ƙungiyar ta umarci shugabanninta na ƙasa da na jihohi da su fara shirya ma’aikata domin yajin aikin, wanda zai fara da tsakar daren Juma’a, 2 ga Oktoba, kuma ya ƙare ranar Lahadi, 4 ga Oktoba.
Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Oktoba 2026, wadda sakataren JNPSNC na kasa, Olowoyo Gbenga, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen amsa buƙatun da ta gabatar wa Shugaba Bola Tinubu a wasiƙar ranar 21 ga Satumba 2026.
Ƙungiyar ta bukaci ma’aikatan gwamnati na tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi su shiga yajin aikin, tana mai cewa ma’aikata da iyalansu na fuskantar matsananciyar wahalar tattalin arziki da ta shafi walwalar rayuwarsu.
Kazalika, JNPSNC ta ce yanayin tattalin arzikin da kuma matsin rayuwa na kara tsananta, lamarin da ta bayyana a matsayin mai wahala da kuma sanya ma’aikata cikin damuwa da takaici.
Buƙatun ƙungiyar sun haɗa da rage farashin litar man fetur zuwa Naira 500, bayar da tallafin albashi ga ma’aikata nan take, da kuma kafa kwamitin haɗin gwiwa domin fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kafin shekarar 2027.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa hauhawar farashin kayayyakin masarufi, sufuri da sauran abubuwan bukatun yau da kullum na kara rage ƙarfin sayayya ga ma’aikata, inda ta umarci shugabanninta da su gaggauta wayar da kan ma’aikata tare da shirya su domin yajin aikin da aka ayyana.
