Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Musulman Nijeriya da su haɗa kai domin kare ’yancinsu na gudanar da addinin Musulunci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sarkin ya yi wannan kiran ne a wajen babban taron majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce taron na da muhimmanci musamman ganin cewa an shafe kusan shekaru bakwai tun bayan gudanar da babban taron majalisar na ƙarshe.
Sarkin Musulmi ya bayyana cewa taron ya ba shugabannin Musulmi daga sassan Nijeriya damar musayar ra’ayoyi da ƙarfafa zumunci a matsayin al’umma ɗaya.
Ya bukaci Musulmi da kada su kasance masu shiru idan batutuwan da suka shafi addininsu da walwalarsu suka taso, yana mai cewa ya kamata su tunkari irin waɗannan batutuwa cikin hikima tare da mutunta haƙƙin sauran mutane.
Ya kuma ce Musulmi ba sa neman tilasta wa kowa shiga Musulunci, yana mai jaddada cewa addinin ya tanadi cewa babu tilastawa a addini.
Ya bukaci Musulmi da su taimaka wa mutanen da suka karɓi Musulunci da son ransu wajen gudanar da addininsu.
Sarkin ya kuma yi kira ga shugabannin Musulmi da sauran al’umma da su kasance masu tawali’u, daidaito da hidima ga bil’adama, yana cewa darajar mutum a wajen Allah tana da alaƙa da tsoronsa ga Allah.
