Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da suke samu, tare da samar da damarmaki na bunƙasa ababen more rayuwa da inganta ayyukan gwamnati.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Bauchi, lokacin da ya karɓi bakuncin ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙin kasa, Taiwo Oyedele, da ministan lafiya Farfesa Ali Pate, waɗanda suka kai masa ziyara.
Gwamnan ya ce gwamnatocin jihohi ba sa adawa da duk wani mataki na gwamnatin tarayya saboda kawai su yi adawa, yana mai cewa idan sun ga abin da suka yi imanin cewa yana da amfani, za su bayyana hakan.
A cewarsa, gyare-gyaren da shugaban Nijeria Tinubu ya aiwatar, musamman a fannin kuɗi da tattalin arziki, sun sa jihohi ke samun ƙarin albarkatun da za su iya amfani da su wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
Bala Mohammed ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya kan matakan da take ɗauka a fannin kiwon lafiya, musamman gina cibiyoyin tantance cututtuka da sauran muhimman ababen more rayuwa na kiwon lafiya a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da gwamnatocin jihohi zai taimaka wajen faɗaɗa damar ’yan kasar na samun ingantaccen kiwon lafiya, tare da inganta rayuwarsu.
Gwamnan ya kuma nuna godiyarsa ga shugaba Tinubu kan matakan da aka ɗauka wajen ƙarfafa tsaro a jihar Bauchi, musamman kafa sabbin bataliyoyin soji a ƙananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa.
A cewarsa, matakan tsaro da gwamnatin tarayya ta ɗauka sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya a wasu yankunan jihar, tare da ba wa mutanen da suka bar gidajensu saboda matsalar tsaro damar komawa garuruwansu.
Bala Mohammed ya ce a lokacin da matsalar ’yan bindiga ta yi tsanani a jihar, ya kai ƙorafinsa ga shugaban kasa, wanda daga bisani ya tura jami’an tsaro da dama domin taimakawa wajen shawo kan matsalar.
Ya tabbatar wa ministocin cewa gwamnatin jihar Bauchi a shirye take ta ƙara haɗin gwiwa da gwamnati domin inganta rayuwar al’ummar jihar da kuma tabbatar da cewa ayyukan ci gaba sun kai ga jama’a.
A nasa ɓangaren, ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, ya ce tawagar ta je Bauchi ne domin ƙaddamar da wasu manyan ayyukan kiwon lafiya da gwamnatin tarayya ta kammala a jihar.
Pate ya ce daga cikin ayyukan akwai wata babbar cibiyar radiodiagnostic da aka gina a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, wadda aka samar domin ƙara inganta ayyukan gano cututtuka ta hanyar amfani da na’urorin zamani.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin radiodiagnostic guda 10 a sassan Nijeriya domin faɗaɗa damar jama’a na samun ingantattun ayyukan gano cututtuka.
