Gwamnonin jam’iyyar APC shida na shiyyar Arewa ta Tsakiya sun amince da sake zaɓen Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a babban zaɓen shekarar 2027.
An bayyana amincewar ne a ranar Asabar yayin wani gangami da aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, wanda ya samu halartar shugabannin APC da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda kuma shi ne babban majiɓincin ƙungiyar North Central Grassroots Mobilisation Network for Tinubu/Shettima 2027, ne ya gabatar da shawarar cewa Tinubu ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa tilo da yankin zai mara wa baya a zaɓen mai zuwa.
Premium Times ta ruwaito cewa, Akume ya buƙaci shugabannin siyasa su mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, yana mai cewa ya kamata a bai wa Tinubu damar kammala wa’adin mulki na shekaru takwas.
Ya ce tsarin ya samo asali ne daga fahimtar da shugabannin siyasa suka cimma a Kaduna a shekarar 1999 domin samar da daidaito tsakanin yankunan biyu.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya goyi bayan shawarar Akume a madadin sauran gwamnonin APC na yankin.
Sule ya ce sun amince da sake zaɓen Tinubu da Shettima ne saboda abin da ya bayyana a matsayin ci gaba a samar da ɗanyen mai, ajiyar kuɗin waje, jari da ayyukan more rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.
Ya kuma ambaci Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND) da manyan ayyukan gine-gine a matsayin wasu daga cikin dalilan da suka sa suke goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasar.
A nasa jawabin, Akume ya kare manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, ƙara kuɗaɗen da ake bai wa jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma zuba jari a fannin ilimi da ayyukan more rayuwa.
Ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin matakin da ke buƙatar jarumtar siyasa, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a yi alkawarin dawo da tallafin ba tare da la’akari da tasirin hakan ga tattalin arziki ba.
Akume ya kuma ambaci babbar hanyar bakin teku ta Legas zuwa Kalaba da kuma shirin gina hanyar Badagry zuwa Sakkwato a matsayin ayyukan da, a cewarsa, za su inganta zirga-zirga da samar da damar tattalin arziki.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci mazauna Arewa ta Tsakiya su goyi bayan Tinubu da jam’iyyar a zaɓen 2027. Ya kuma yi iƙirarin cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa yankin abubuwan da suka wuce na gwamnatocin baya.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta isar da saƙon fatan alheri na mijinta ga yankin, inda ta jaddada cewa gwamnatin tana mai da hankali kan tsaro, haɗin kan ƙasa da bunƙasar tattalin arziki.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne sakataren kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu, shi ma ya tabbatar da cewa APC za ta ci gaba da tattara goyon baya domin sake zaɓen shugaban ƙasar.
Sanarwar ta ce gwamnonin APC shida na Arewa ta Tsakiya sun yi alƙawarin yin aiki domin sake zaɓen Tinubu da Shettima, da kuma samun nasarar ’yan takarar jam’iyyar a sauran matakan gwamnati.
Sai dai sanarwar da aka bayar kan amincewar ba ta ƙunshi adadin ƙuri’un kowane gwamna ko cikakken bayani kan wata takardar amincewa da gwamnonin suka sanya wa hannu ba.
