Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta nesanta kanta tare da yin watsi da wani jerin sunayen ’yan takarar gwamna na ƙarya da ke yawo a shafukan sada zumunta gabanin babban zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta a ranar Litinin, INEC ta bayyana cewa wannan takarda ta bogi ce kuma ba daga gare ta ta fito ba, tana mai gargaɗin al’umma da su yi watsi da ita tare da daina yaɗa ta.
Jerin sunayen na ƙaryar ya shafi ’yan takarar gwamna a jihohi shida da suka haɗa da Kano, Zamfara, Gombe, Yobe, Plateau, da kuma Delta.
INEC ta jaddada cewa babu wata sanarwa ta musamman da ta fitar da ta shafi sauye-sauye a jerin sunayen ’yan takarar gwamna a waɗannan jihohi shida, inda ta buƙaci al’umma da su riƙa samun ingantattun bayanai daga shafukanta na intanet da dandalin sada zumunta da ke da shaidar tantancewa.
Wannan gargaɗi na INEC na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumar ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamna na zaɓen farkon shekara mai zuwa, lamarin da ya haifar da korafe-korafe da ce-ce-ku-ce a wasu jihohi sakamakon rashin ganin sunayen wasu ’yan takara a jerin.
