Almajirai a jihar Jigawa sun koka kan karancin abincin sadaka da suke samu daga mazauna yankunansu, lamarin da ke tilasta wa wasu daga cikinsu gudanar da wasu ƙananan ayyuka domin samun abincin da za su ci, sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa binciken da wakilanta na Arewa suka gudanar a Dutse da wasu manyan garuruwan jihar ya nuna cewa al’adar bayar da abinci kyauta ga almajirai na fuskantar koma baya saboda matsin tattalin arziki.
A al’adance, almajirai da dama da ke karatun Alƙur’ani a makarantun allo, waɗanda ake kira Tsangaya, sun dogara ne da abincin da mazauna yankunan da suke karatu ke ba su kyauta domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Sai dai rahoton ya nuna cewa tsadar rayuwa ta rage ikon iyalai wajen bayar da abinci ga almajirai, yayin da wasu gidaje ke kokawa kan yadda za su ciyar da nasu yaran.
Wannan hali ya sa wasu almajirai fara neman wasu hanyoyin samun abinci, ciki har da ɗaukar ciyawa zuwa wuraren kiwon dabbobi, ɗebo ruwa, ɗaukar itacen girki da kuma yin wasu ayyukan gida domin a ba su abinci.
Wani almajiri mai shekaru 12, Musa Ibrahim, da ke karatu a wata makarantar Tsangaya a unguwar Danmasara da ke Dutse, ya ce ya koma gyara da wankin takalma domin samun abin da zai ci.
Musa ya bayyana cewa a baya suna samun abinci cikin sauƙi daga gidajen jama’a, amma yanzu wasu na gaya musu cewa babu abincin da za su ba su.
Ya ce wani lokaci suna zagayawa tun safe har rana ba tare da sun samu abin ci ba.
Haka kuma, wani almajiri mai shekaru 10, Sani Umar, da ke unguwar Yalwawa a Dutse, ya ce yanzu yana zuwa neman ciyawa domin masu kiwon dabbobi su ba shi abinci.
A nasa ɓangaren, Abubakar Dahiru, mai shekaru 13 daga garin Shuwarin, ya ce yana wanke kwanoni da ɗebo ruwa ga mazauna yankinsu da gidajen cin abinci domin samun abinci.
Wani mazaunin Dutse, Aliyu Ashiru, ya bayyana damuwarsa kan wannan yanayi, yana mai cewa a baya al’ummar yankin sun saba ba almajirai abinci, amma yanzu tsadar rayuwa ta sa ciyar da iyalai ma ya zama ƙalubale.
Ita ma Maryam Salisu, mazauniyar unguwar Takur-site, ta buƙaci gwamnati da sauran masu hannu da shuni su taimaka wa yaran, tana mai cewa bai kamata a bar su suna yawo tsawon yini suna neman abinci ba.
Shugaban wata makarantar Tsangaya da ke kusa da ƙauyen Sakwaya a Dutse, Malam Isa Mohammad, wanda ke kula da almajirai sama da 80, ya ce matsalar rashin abinci na shafar karatunsu.
A cewarsa, wasu yaran na fita da safe neman abinci kuma su dawo da yamma, lamarin da ke rage lokacin karatu da haddar Alƙur’ani.
Wani shugaban makarantar Tsangaya a Birnin Kudu, Alaramma Audu Haruna, shi ma ya ce ciyar da almajirai ya zama babban nauyi, saboda taimakon abinci da suke samu daga jama’a ya ragu sosai.
