DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 16, 2026
HomeWasanniReal Madrid ta bukaci shugaban La Liga ya gaggauta yin murabus

Real Madrid ta bukaci shugaban La Liga ya gaggauta yin murabus

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta buƙaci shugaban gasar La Liga ta Sifaniya, Javier Tebas, da ya yi murabus nan take daga muƙamansa na shugaban La Liga da mataimakin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, sakamakon kalaman da ya yi kan yadda ƙungiyar ke gudanar da yaɗa bayananta.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, Real Madrid ta bayyana kalaman Tebas a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da cewa suna da matuƙar muni.

Ƙungiyar ta ce kwatanta hanyoyin sadarwarta da dabarun farfagandar Nazi a lokacin yaƙin duniya na biyu babban cin mutunci ne ga shugabancinta da kafar talabijin ɗinta.

Tebas ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa shugabancin Real Madrid na jagorantar masu magana da yawunta, yayin da gidan talabijin ɗin ƙungiyar ke jagorantar yaɗa saƙonninta.

Jaridar Punch ta ruwaito ya kuma zargi ƙungiyar da zaɓar abubuwan da suka dace da ita, maimaita korafe-korafe da kuma haifar da shakku domin gina labarin da take son jama’a su yarda da shi.

Shugaban na La Liga ya kwatanta waɗannan dabaru da hanyoyin farfagandar Joseph Goebbels, tsohon ministan farfagandar Nazi ta Jamus, wanda ya yi amfani da maimaita saƙonni da nuna wasu a matsayin maƙiya domin rinjayar ra’ayin jama’a.

Sai dai Tebas ya jaddada cewa kwatancen nasa ya shafi dabarun yaɗa saƙonni ne kawai, ba akidar Nazi ko magoya bayan Real Madrid ba.

Duk da wannan bayani, Real Madrid ta yi watsi da bambancin da Tebas ya yi, tana mai cewa kalamansa wani sabon salo ne na hare-haren da yake kai wa ƙungiyar, shugabanta da kafafen yaɗa labaranta.

Ƙungiyar ta kuma danganta takaddamar da batun Negreira, wanda ya shafi kuɗaɗen da Barcelona ta biya tsawon shekaru ga wani tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalin wasa na Sifaniya.

Real Madrid ta bayyana cewa ta riga ta tuntuɓi hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, domin neman cikakken bincike kan kuɗaɗen da Barcelona ta biya.

Ta kuma buƙaci a sake fasalin tsarin alkalanci da wasu sassan hukumomin ƙwallon ƙafa, tana mai cewa rashin martanin hukumomin da Tebas ke jagoranta ko wakilta kan batun ya jawo damuwa.

A ƙarshe, Real Madrid ta ce kalaman Tebas sun nuna rashin tsaka-tsaki, girmamawa da adalci da ake buƙata daga wanda ke riƙe da muƙaman jagoranci a ƙwallon ƙafa.

Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci ya yi murabus nan take daga shugabancin La Liga da mataimakin shugabancin hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata