DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 16, 2026
HomeLabaraiAmnesty International na jan hankalin gwamnatin Nijeriya kan yara 42 da aka...

Amnesty International na jan hankalin gwamnatin Nijeriya kan yara 42 da aka sace a Borno

Yara 42 ’yan makaranta daga ƙaramar hukumar Askira Uba ta jihar Borno, sun kwashe kwanaki 153 a hannun ’yan bindiga tun bayan sace su a ranar 15 ga Mayun 2026, yayin da ake ci gaba da samun rahotannin sace wasu mutane a sassan Arewacin Nijeriya.

Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana cewa babu wani yaro da ya kamata ya shiga irin halin da yara ke ciki a Nijeriya a yanzu, kuma bai kamata neman ilimi ya zama hanyar shiga irin wannan mummunan yanayi ba.

Amnesty ta ce Nijeriya ta sake gaza wa wajen kare yaran ƙasar ta hanya mai matuƙar ban tsoro.

Ƙungiyar Amnesty ta ƙara da cewa makomar dubban yaran makarantu a Arewacin Nijeriya na cikin duhu, sakamakon rufe ɗaruruwan makarantu har sai baba-ta-gani a wasu jihohi saboda ƙaruwar matsalolin tsaro.

Haka kuma, wasu yara sun daina zuwa makaranta sakamakon raunin tunani da suka samu bayan shaida hare-haren ta’addanci ko kuma zaman da suka yi a hannun masu garkuwa da mutane.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin Nijeriya ta ƙara ƙaimi wajen ceto dukkan yaran da ke hannun masu garkuwa cikin aminci da tsaro, tare da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ake zargi da aikata laifukan.

Wannan bukata ta Amnesty International ga gwamnatin Nijeriya ta zo ne rana guda da umarnin Shugaba Tinubu ga shugabannin tsaron ƙasar da kada su bar sansanin ’yan ta’adda ko ɗaya, har sai sun ceto duk waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ne ya isar da sakon shugaban yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, jim kaɗan bayan kammala wani babban taron tsaro na musamman da Tinubu ya jagoranta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata