Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓensa a jihohi 12 kacal, yayin da shugabannin jam’iyyar APC za su wakilce shi a jihohi sama da 20 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jadawalin gangamin da jam’iyyar ta fitar ya nuna cewa za a fara gangamin ne a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoba, 2026, yayin da ake sa ran kammala rangadin gangamin shugaban a Legas ranar 9 ga Janairu, 2027.
Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan gangamin yaƙin neman zaɓe ba saboda akwai buƙatar ya daidaita harkokin siyasa da nauyin gudanar da gwamnati.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce har yanzu akwai nauye-nauyen da yake da alhakin saukewa a wuyansa.
Sai dai ya yi alƙawarin samar da lokacin da zai yi magana kai tsaye da ’yan Nijeriya domin neman goyon bayansu a zaɓen 2027.
Jadawalin ya nuna cewa Tinubu ba zai halarci gangamin APC a Cross River ranar 2 ga Nuwamba, Gombe ranar 3 ga Nuwamba, Nasarawa ranar 4 ga Nuwamba da Ekiti ranar 5 ga Nuwamba ba.
Haka kuma, ba zai halarci gangamin a Ebonyi, Jigawa, Ondo da Edo ba, waɗanda aka tsara gudanarwa tsakanin 9 zuwa 12 ga Nuwamba.
Sai dai zai halarci gangamin a jihar Rivers ranar 7 ga Nuwamba, sannan ya koma Plateau ranar 14 ga Nuwamba.
Haka kuma, shugaban ba zai halarci gangamin APC a Yobe, Kebbi, Akwa Ibom da Anambra ba, waɗanda aka tsara gudanarwa tsakanin 16 zuwa 19 ga Nuwamba.
Zai halarci gangamin a Oyo ranar 21 ga Nuwamba, yayin da aka tsara gudanar da sauran gangamin a Borno ranar 25 ga Nuwamba, Enugu ranar 28 ga Nuwamba da Bauchi ranar 29 ga Nuwamba.
Za a ci gaba da gangamin a watan Disamba, ciki har da Sokoto ranar 5 ga Disamba, Delta ranar 12 ga Disamba da Kano ranar 17 ga Disamba.
Sai dai jam’iyyun adawa sun yi suka kan shirin shugaban na rashin halartar gangamin a wasu jihohi, inda jam’iyyar APM ta buƙaci Tinubu ya halarci gangamin a dukkan jihohin ƙasar ko kuma ya janye takararsa.
Jam’iyyar ta danganta rashin halartar gangamin da batun lafiyar shugaban, duk da cewa Tinubu ya ce dalilin shi ne nauyin gudanar da gwamnati.
