Dakarun haɗin gwiwa na rundunar Operation Fansan Yamma ta Arewa maso Yamma sun samu nasarar hallaka ’yan ta’adda biyu, tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda huɗu da babura takwas a yayin wasu jerin sumame a jihar Sakkwato.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Aliyu Danja ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an gudanar da ayyukan ne ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026.
Ya ce yayin aikin, dakarun runduna ta biyu sun yi arangama da ’yan ta’adda a dajin Waria, inda suka yi musayar wuta da su tare da kashe ɗaya daga cikinsu.
A cewarsa, sojojin sun ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu da babura biyu a yayin arangamar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Danja ya ƙara da cewa, bayan ci gaba da bincike a yankin, dakarun sun sake ƙwato wasu babura shida, bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai masu rai guda huɗu, harsasai 23 da na’urar sadarwa.
Wannan ya kai adadin bindigogin AK-47 da aka ƙwato zuwa huɗu, yayin da adadin baburan ya kai takwas.
Ya ce nasarorin da aka samu sun nuna ƙudurin dakarun Operation Fansan Yamma na wargaza hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankunan da suke gudanar da ayyukansu.
Ya kuma yaba wa al’umma bisa ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin kai ga hukumomin tsaro.
Rundunar ta buƙaci mazauna yankunan da su ci gaba da sanya ido tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro mafi kusa da su duk wani motsi ko aiki da suke zargi, domin taimakawa ayyukan sojojin da ke gudana.
