Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya bayyana cewa ba zai nemi ci gaba da zama a kan karagar mulki ba bayan wa’adinsa na yanzu ya ƙare a shekarar 2030, yana mai cewa an riga an kammala wannan batu ba tare da wata tantama ba.
Sisi, mai shekaru 71, tsohon janar ne a rundunar sojin ƙasar, wanda ya zama shugaban Masar a shekarar 2014. Ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen bikin yaye ɗalibai a makarantar horas da sojoji ta Masar, da ke sabon babban birnin gudanarwa na ƙasar, ɗaya daga cikin manyan ayyukan raya ƙasa da ya sa a gaba.
Da yake jawabi ga waɗanda aka yaye da jami’an gwamnati a sabon birnin da ke gabashin Alkahira, Sisi ya ce ba za a taɓa kundin tsarin mulkin ƙasar ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce, “Lokacin da ya rage kafin shekarar 2030 shi ne ƙarshen wa’adina na shugaban ƙasa, idan har ina da rai. An riga an kammala wannan batu, kuma babu wata tattaunawa a kansa.”
Kundin tsarin mulkin Masar da aka amince da shi a shekarar 2014, bayan hambarar da tsohon shugaban ƙasar mai bin tafarkin Musulunci, Mohamed Morsi, ta hannun sojoji a shekarar 2013, ya tanadi cewa shugaban ƙasa zai yi wa’adi biyu ne kawai, kowannensu na shekaru huɗu.
Sai dai gyare-gyaren kundin tsarin mulkin da aka amince da su a wani zaɓen raba gardama a shekarar 2019 sun ƙara wa’adin shugaban ƙasa daga shekaru huɗu zuwa shida, tare da tanade-tanaden wucin gadi da suka ba Sisi damar sake tsayawa takara na wani wa’adi.
A ƙarƙashin waɗannan gyare-gyare, an sake zaɓen Sisi a shekarar 2023 domin wa’adin shekaru shida, wanda zai ƙare a shekarar 2030.
Masu suka da wasu ’yan adawa sun daɗe suna hasashen yiwuwar sake yin wasu gyare-gyaren kundin tsarin mulkin da za su iya ba shi damar ci gaba da mulki bayan 2030.
Kafin ya tsaya takarar shugaban ƙasa, Sisi ya taɓa musanta cewa yana da burin shiga siyasa. Sai dai ya yi murabus daga mukaminsa na ministan tsaro a shekarar 2014, sannan ya shiga takarar shugaban ƙasa, inda ya samu nasara.
A jawabin nasa na ranar Asabar, Sisi ya ce za a yi amfani da shekarun da suka rage kafin 2030 wajen shirya sabbin shugabanni, inda makarantar horas da sojojin za ta ci gaba da horas da ɗaruruwan mutane da ake shirin ba wa mukaman gwamnati, ministoci da kuma masu yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa, kan shugabanci da gudanar da mulki.
A tsawon shekaru 12 da ya yi kan karagar mulki, Sisi ya jagoranci wani gagarumin shirin raya ƙasa da gwamnati ke jagoranta, wanda ya fi mayar da hankali kan manyan ayyukan gine-gine da samar da ababen more rayuwa.
Sai dai masu sukar gwamnatin sun ce an gudanar da yawancin waɗannan ayyuka ne ta hanyar karɓar bashi mai yawa, lamarin da ya taimaka wajen ƙara nauyin bashin da Masar ke ciki, tare da tsananta matsin tattalin arzikin ƙasar.
Haka kuma, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa sun ci gaba da sukar gwamnatin Sisi kan takaita ayyukan ’yan adawa, ƙungiyoyin farar hula da ’yancin faɗar albarkacin baki.
Sai dai gwamnatin Masar ta ƙi amincewa da waɗannan zarge-zarge, tana mai cewa matakan da take ɗauka sun zama dole domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.
