DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 15, 2026
HomeLabaraiDino Melaye ya zargi majalisar dokoki da gazawa wajen sa ido kan...

Dino Melaye ya zargi majalisar dokoki da gazawa wajen sa ido kan gwamnatin Tinubu

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya zargi shugabannin majalisar dokokin Nijeriya ta 10 da kasa gudanar da cikakken aikin sa ido kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan na bai wa shugaban ƙasar damar amfani da ikon zartarwa ba tare da isasshen bincike daga majalisa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Melaye ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya yi nazari kan ayyukan majalisar tare da tambayar ko tana gudanar da aikinta cikin ’yancin da kundin tsarin mulki ya ba ta.

Melaye, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC, ya yi suka ta musamman ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kan yadda suka tafiyar da batutuwan gyaran dokokin zaɓe, aiwatar da kasafin kuɗi, gyaran kundin tsarin mulki da sauran manufofin gwamnatin tarayya.

Ya ce aikin majalisa bai tsaya ga amincewa da ƙudirin doka ko shawarwarin gwamnati kawai ba, domin wajibi ne ta binciki matakan da shugaban ƙasa ke ɗauka tare da tabbatar da cewa suna cikin iyakokin kundin tsarin mulki.

Melaye ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin majalisa da gwamnati ba yana nufin mika wuya ba ne, yana mai cewa ya kamata majalisa ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ’yanci, musamman a lokacin da ake buƙatar ta binciki matakan ɓangaren zartarwa.

Tsohon sanatan ya kawo misalin gyaran dokar ’yan sandan Nijeriya da aka yi a watan Yulin 2024, wanda ya ba Sufeto-Janar na ’yan sanda damar ci gaba da riƙe muƙaminsa har zuwa ƙarshen wa’adin da aka bayyana a wasiƙar naɗinsa, duk da ƙa’idojin ritayar jami’an ’yan sanda.

A cewarsa, abin da ya jawo tambayoyi shi ne yadda aka gabatar da ƙudirin gyaran dokar, sannan majalisun biyu suka karanta tare da amincewa da shi a matakai na farko, na biyu da na uku a rana guda.

Melaye ya ce saurin amincewa da ƙudirin ya haifar da tambayoyi kan ko an gudanar da isasshen nazari kafin a amince da dokar da ta shafi wa’adin shugaban rundunar ’yan sanda.

Ya kuma bayyana cewa gyaran dokar ya fara amfani ga tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, wanda a baya ya taɓa zama babban jami’in tsaron Tinubu lokacin da yake gwamnan jihar Legas.

Rahoton ya ce Egbetokun ya bar muƙaminsa a watan Fabrairun 2026, inda Olatunji Disu ya gaje shi.

Melaye ya kuma yi nuni da cewa Disu ya taɓa zama mataimakin Tinubu mai kula da harkokin tsaro lokacin da yake gwamnan Legas, sai dai ya amince cewa waɗannan alaƙa kaɗai ba su tabbatar da aikata ba daidai ba ko yin maguɗin zaɓe ba.

Melaye ya kuma yi tambayoyi kan yadda majalisar dokoki ta gudanar da batun ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers a watan Maris na 2025, musamman ko tsarin kaɗa ƙuri’ar da aka yi a majalisun biyu ya cika sharadin samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na dukkan mambobin majalisa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Dangane da takaddamar dokar zaɓe ta 2026, ya soki yadda majalisar wakilai ta gudanar da batun janye matsayinta na baya kan wajabcin aika sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura a ainihin lokacin da aka kammala kaɗa ƙuri’a.

Majalisar wakilai ta amince da wannan tanadi a watan Disamban 2025, amma daga baya ’yan majalisar suka sake duba matsayarsu a watan Fabrairun 2026.

Rahoton ya ce batun ya haifar da zanga-zanga da hargitsi a zauren majalisar kafin gudanar da zaman sirri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata