DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 17, 2026
HomeBabban Labari Sojoji kadai ba za su iya kawo karshen ‘yan bindiga a Nijeriya...

Sojoji kadai ba za su iya kawo karshen ‘yan bindiga a Nijeriya ba – Ribadu

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ayyukan soji kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga a kasar ba, yana mai buƙatar ƙarfafa musayar bayanan sirri, tsaron iyakoki da sa hannun al’umma wajen yaƙi da rashin tsaro.

Ribadu ya ce matsalar ’yan bindiga ta wuce satar shanu, fashi a kan manyan tituna da garkuwa da mutane, inda ta kai ga mamaye yankuna, karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba daga al’ummomin karkara da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne ta bakin Daraktan Sashen Shari’a a ofishinsa, Zakari Mijinyawa, a wani taron tattaunawa kan hanyoyin tunkarar matsalar ’yan bindiga da ƙungiyar ‘Sokoto Advancement Forum’ ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ranar Asabar.

Ribadu, ya ce kusancin jihar Sakkwato da jamhuriyar Nijar da kuma yankin Sahel ya ƙara wa matsalar rashin tsaro siffar ta ƙetare iyakokin ƙasa, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke cin gajiyar iyakoki marasa tsaro da giɓin da ke cikin tsarin tsaro domin ci gaba da ayyukansu.

“Saboda haka, dole ne mu haɗa ayyukan tsaro da bayanan sirri, ingantaccen kula da iyakoki, haɗin gwiwar ƙasashen yankin da kuma ci gaba da ɗaukar matakai kan safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba da sauran kayan tallafa wa ayyukan ta’addanci.”

Ya kuma yi kira da a ɗauki matakan magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke sa matasa zama masu sauƙin shiga ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Haka kuma, ya buƙaci samar da shirye-shiryen gyara da sake shigar da mutanen da suka cancanta cikin al’umma, bisa ƙa’ida, ga waɗanda suke shirye su yi watsi da tashin hankali.

Ribadu ya bayyana muhimman fannoni guda biyar da ya kamata a mayar da hankali a kai domin inganta tsaro a Sakkwato. Su ne hana ’yan bindiga samun mafaka, ƙarfafa tattara bayanan sirri da tsarin gargaɗin farko, gina amincewa tsakanin jami’an tsaro da al’umma, kare noma da hanyoyin dogaro da kai na mazauna karkara, da kuma hana ɗaukar matasa cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Ya buƙaci hukumomin tsaro su inganta haɗin gwiwa da musayar bayanai, yana mai cewa al’umma za ta fi son bayar da bayanan sirri idan ta amince cewa hukumomin tsaro za su ɗauki mataki yadda ya kamata tare da kare sirrin bayanan da aka ba su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata