Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano na fatan tara harajin Naira biliyan 1.5 daga allunan talla...

Gwamnatin Kano na fatan tara harajin Naira biliyan 1.5 daga allunan talla da ababen hawa a jihar

Sabuwar hukumar kula da tallace-tallace ta jihar Kano ta bayyana shirin samar da akalla Naira biliyan 1.5 na kudaden shiga ga gwamnati.

 

Yayin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan ta, shugaban hukumar Kabiru Dakata ya ce za su tara kudaden ne daga watan Satumba zuwa Disambar 2025.

 

Ya kara da cewa shirye-shiryen hukumar sun kankama na ganin an cimma wannan adadi, tare da bayyana fatan samar da Naira biliyan 3 a 2026 da kuma biliyan 5 a 2027, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

 

A cewar sa, gwamnatin Kano ta kafa hukumar ne ba don tara haraji ba kawai, har ma da tsaftace ayyukan talla a fadin jihar, domin gogayya da wuraren da suka ci-gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata