Kansila mai wakiltar mazabar Kinkiba da ke karamar hukumar Soba a jihar Kaduna, Sunusi Hashim, ya nada masu bashi shawara 18.
A cewar kansilan, ya dauki wannan mataki ne domin karfafa shugabancinsa, kana ya zabo su ne dogaro da irin rawar suke takawa wajen ci-gaban al’ummar yankin.
Taron nadin mataimakan nasa ya gudana ne a ranar Lahadi, inda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, sarakunan gargajiya da kuma sauran al’umma, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
