Tsohon gwamnan Jihar Kano, kuma Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan yadda Shugaban Amurka Donald Trump ke ta yin maganganu masu tsanani kan Nijeriya, bayan sanya ta cikin jerin kasashen da ake kiran “ƙasashe masu damuwa ta musamman.”
Kwankwaso ya ce Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yancin kanta, wacce matsalolinta na tsaro ba su da alaƙa da addini ko kabila. Sannan kuma zai fi dacewa Amurka ta taimaka da sabbin fasahohi wajen yaki da ‘yan ta’adda, maimakon yin barazana da ka iya rarraba ƙasar.
Kwankwaso ya kuma bukaci gwamnati ta nada jakadu na musamman domin tattaunawa da gwamnatin Amurka, tare da tabbatar da jakadun dindindin don kare muradun Nijeriya a kasashen waje.
A karshe, Kwankwaso ya kira ‘yan Nijeriya da su hada kai a wannan lokaci maimakon rarrabuwa sannan yana mai yi ma kasar fatan alheri.
