Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Dr. Bernard Doro da Dr. Kingsley Udeh a matsayin sababbin ministoci, kafin fara zaman majalisar zartarwa na farko tun watan Yuli.
Dr. Doro, kwararren likita daga Filato, ya maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda, yayin da Dr. Udeh daga Enugu ya maye gurbin Uche Nnaji wanda ya yi murabus kan takardun karatu.
Bayan rantsuwar, Tinubu ya jagoranci zaman majalisar inda ministan kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa dawowar Nijeriya kasuwar lamuni ta duniya ta jawo karuwar sha’awar masu saka jari, inda kudin Eurobond ya samu karin bukata mai yawa.
Edun ya ce gwamnati za ta cigaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ta inganta kasuwanci, da tabbatar da rarraba ribar ci-gaba ga ’yan kasa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



