Monday, April 6, 2026
HomeKetareTrump ya sha alwashin fara korar bakin haure daga Amurka a rana...

Trump ya sha alwashin fara korar bakin haure daga Amurka a rana ta farko da ya kama aiki

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na korar miliyoyin bakin hauren da ba su da takardun izinin zama a kasar.

Baya ga haka, Trump ya ce zai sanya haraji kan kasashen ketare da ke huldar kasuwanci da kasar Amurka da kuma yin afuwa ga mutanen da aka yankewa hukunci saboda kutsawa a ginin majalisar kasar “Capitol” a ranar 6 ga Janairun shekarar 2021. 

Trump ya sanar da wadannan tsare-tsaren ne lokacin da ya ke bayyana ajandojin gwamnatinsa, a yayin wata hira da gidan talabijin na NBC news.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata