DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasa'Tausayi ya sa na amince na yi takara tare da Peter Obi...

‘Tausayi ya sa na amince na yi takara tare da Peter Obi a 2023’

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa tausayi da ya ji wa Peter Obi da kuma halin da Nijeriya ke ciki ne suka sa ya amince ya tsaya takara tare da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ba wai saboda daidaituwar manufofinsu ta siyasa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Datti ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Symfoni, inda ya ce kafin ya amince da tayin, Peter Obi ya tuntuɓi wasu manyan ‘yan siyasa uku domin su kasance abokan takararsa amma suka ƙi amincewa.

Datti ya ce ya ji tausayin Obi da kuma Nijeriya, lamarin da ya sa ya shiga takarar a matsayin wanda yake son taimakawa ƙasa. Ya ce da ma yana daga cikin mutanen da ke shiga harkokin ƙasa bisa son rai domin ci gaban Nijeriya.

A cewarsa, mutane da dama sun yi tunanin zai ci gaba da bin tafarkin siyasar Peter Obi bayan zaɓen 2023, amma ya ce goyon bayan da ya ba shi yana da iyaka. Ya jaddada cewa Peter Obi ba shi da iko kan makomar siyasarsa.

Tsohon sanatan ya kuma yi tsokaci kan ficewar Peter Obi daga Labour Party, yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida ba su isa su zama dalilin barin jam’iyya ba. Ya tambayi me ya sa Obi ke ganin matsalolin da ya ce sun addabi LP ba za su sake tasowa a sabbin jam’iyyun da ya koma ba.

Datti, wanda ya fice daga Labour Party zuwa jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a watan Mayun 2026, ya ce ya kamata a gyara matsalolin cikin gida maimakon yin watsi da su da komawa wata jam’iyya.

Kalaman na Datti na zuwa ne a lokacin da Peter Obi ya sauya sheƙa zuwa wasu sabbin ƙungiyoyin siyasa, lamarin da ya ƙara jawo muhawara tsakanin magoya bayansu gabanin zaɓen 2027.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata