Ƙungiyar Daliban Nijeriya (NANS) reshen shiyyar Arewa maso Gabas ta umarci mambobinta su fito zanga-zangar lumana domin nuna goyon baya ga ɗalibai 42 da aka sace daga Makarantar Government Day Secondary School da ke Mussa a ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.
A cewar wata sanarwa da jaridar Punch ta ruwaito, za a gudanar da zanga-zangar ne daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Yuni, 2026, a jihohin Borno, Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba domin jawo hankalin mahukunta kan halin da ɗaliban ke ciki da kuma neman a ƙara ƙaimi wajen ceto su.
A sanarwar da Babban Sakataren Mai Kula da Ofishin Shiyya na NANS, Lukman Yusuf, ya fitar, ƙungiyar ta ce zanga-zangar za ta nuna alhini da goyon baya ga iyalan ɗaliban tare da matsa wa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro lamba su gaggauta kubutar da su.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa tsaro a makarantu da cibiyoyin ilimi a faɗin ƙasar domin tabbatar da cewa makarantu sun ci gaba da kasancewa wuraren koyo masu aminci ga ɗalibai.
Mai Kula da Shiyyar Arewa maso Gabas a NANS, Kwamared Mu’azu Hina, ya ce akwai buƙatar haɗin kai wajen neman dawo da ɗaliban cikin koshin lafiya da kuma samar da ingantaccen tsaro ga masu neman ilimi a Nijeriya.
Sace ɗaliban 42 daga makarantar da ke Mussa ya tayar da hankalin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, mazauna yankin da ƙungiyoyin farar hula, yayin da ake ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa domin ceto su.
