Jam’iyyar adawa ta ADC a Nijeriya ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wanda ya umarci hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Kotun, ƙarƙashin jagorancin Justice Peter Lifu, ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun ba su cika wasu sharuddan da kundin tsarin mulki da dokar zaɓe suka tanada ba.
Sai dai ADC ta bayyana hukuncin a matsayin yunƙurin amfani da ɓangaren shari’a wajen raunana dimokuraɗiyya da kuma murƙushe jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.
Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce INEC da kanta ta kare matsayin ADC a kotu, tana mai cewa jam’iyyar ta cika dukkan sharuddan da doka ta gindaya kuma babu wani dalili na soke rajistarta.
ADC ta kuma yi zargin cewa kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar duk da umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara na dakatar da ci gaba da shari’ar da aka bayar a ranar 22 ga Mayu, 2026.
Jam’iyyar ta danganta hukuncin da abin da ta kira ƙoƙarin jam’iyyar mai mulki ta APC na raunana adawa domin bai wa Bola Ahmed Tinubu damar samun wa’adi na biyu ba tare da ƙalubale mai ƙarfi ba.
A gefe guda kuma, gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC sun sha musanta zarge-zargen cewa suna ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, suna cewa adawa mai ƙarfi na da muhimmanci ga ci gaban dimokuraɗiyya.
