DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiMajalisar Wakilai ta fara garanbawul kan dokokin aikin soji a Nijeriya

Majalisar Wakilai ta fara garanbawul kan dokokin aikin soji a Nijeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta fara nazarin jerin kudurorin dokoki da ke da nufin sake fasalin tsarin rundunar sojin ƙasar, inganta walwalar jami’ai da tsofaffin sojoji, tare da ƙarfafa ƙarfin rundunar wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro.

Da yake jawabi a taron sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu da Kwamitin Tsaro na Majalisar ya shirya a Abuja, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce kudurorin na da muhimmanci wajen daidaita dokokin soja da sauye-sauyen da ke faruwa a fannin tsaro.

Ya bayyana cewa sabbin ƙalubalen tsaro da suka haɗa da fashin teku a yankin Gulf of Guinea, yaƙin yanar gizo da kuma haɗin gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata manyan laifuka sun nuna buƙatar yin garambawul ga dokokin rundunar sojin Najeriya.

Daga cikin muhimman kudurorin da ake dubawa akwai kudirin Armed Forces Farms and Ranches Scheme Bill, wanda ke da nufin haɗa shirye-shiryen samar da abinci da ayyukan soja, musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

Sauran sun haɗa da kudirin Gender Representation in the Armed Forces Bill domin ƙara wakilcin mata a rundunar soja, da kuma Nigerian Military Force Bill wanda zai soke tsohon Armed Forces Act tare da maye gurbinsa da sabon tsarin gudanarwa da ya dace da buƙatun zamani.

Haka kuma ana nazarin kudirin Veterans’ Federation of Nigeria Bill wanda ke neman inganta walwala da jin daɗin tsofaffin sojojin Najeriya.

Kakakin Majalisar ya yi kira ga jami’an soja masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, ƙungiyoyin farar hula, masu rajin kare haƙƙin mata, lauyoyi da sauran ‘yan ƙasa da su ba da gudummawar ra’ayoyi domin samar da dokokin da za su ƙarfafa tsaro da inganta aikin rundunar soji.

A nasa jawabin, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Babajimi Benson, ya ce taron wata muhimmiyar dama ce ga masu ruwa da tsaki su taimaka wajen tsara dokokin da za su ƙarfafa tsaro, ilimin soja, bincike, kula da lafiya, walwalar tsofaffin sojoji, samar da abinci da kuma daidaiton jinsi a rundunar sojin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata