Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi alkawarin tabbatar wa sanatocin da suka rasa tikitin takarar APC a zabukan fidda gwani samun tikitin takara.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Eseme Eyiboh, ya fitar, an bayyana cewa Akpabio bai yi irin wannan alkawari ba, kuma bai ba kowa izinin yin hakan a madadinsa ba.
Sanarwar ta ce abin da Akpabio ya yi shi ne nuna alhini ga sanatocin da sakamakon zabukan fidda gwani ya shafa tare da tabbatar musu cewa shugabancin APC na kokarin magance matsalolin da suka taso daga tsarin.
Haka kuma, ya sanar da su cewa za a fitar da jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyar na ƙarshe bisa tanadin kundin tsarin APC da dokokin zaɓe.
Dangane da batun tsaro, ofishin Akpabio ya kuma musanta cewa ya nuna adawa da sa ido ko binciken majalisa kan ayyukan rundunar sojoji.
Sai dai ya bayyana cewa a halin yanzu gudanar da bincike a bainar jama’a kan sojoji na iya rage musu ƙwarin gwiwa yayin da suke fafatawa da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar.
Jaridar Punch ta ambato Akpabio ya bukaci kafafen yaɗa labarai da al’umma su yi watsi da rahotannin da ya kira marasa inganci tare da neman ƙarin bayani daga ofishinsa kafin wallafa labaran da suka shafi kalamansa.
