DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiManjo janar Rabe mai ritaya da matarsa sun nemi gwamnati ta ceto...

Manjo janar Rabe mai ritaya da matarsa sun nemi gwamnati ta ceto su a hannun masu garkuwa

Tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe da matarsa, Amina Abubakar, waɗanda aka sace a Jihar Katsina mako guda da ya gabata, sun bayyana a wani sabon bidiyo suna roƙon gwamnati da ta taimaka wajen kuɓutar da su.

A cikin bidiyon da masu garkuwar suka fitar, matar Janar Rabe ta ce masu garkuwar sun buƙaci a saki wasu mutum uku da suka ambata da sunayen Sani, Aminu da Nasiru, tare da mayar musu da dabbobin da ake zargin an kwace musu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika waɗannan buƙatu domin su shaki iskar ‘yanci.

Shi ma Janar Rabe ya yi kira da a nemi hanyar samar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa.

Rahoton ya nuna cewa babu wata buƙatar kuɗin fansa da aka ambata a cikin bidiyon.

An sace Janar Rabe, matarsa da direbansu ne a hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu, bayan wasu ‘yan bindiga sun tare motarsu tare da buɗe musu wuta.

Direban ya samu rauni a hannu wanda yanzu haka yake samun kulawar likita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata