Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna zanga-zanga a fadar Sarkin Musulmi tsohon bidiyo ne, ba sabon abu ba kamar yadda ake yadawa.
A cewar fadar, bidiyon an dauke shi ne tun a shekarar 2024 lokacin da ake samun zanga-zangar da ta shafi tsadar rayuwa a kasar, amma an sake watsa shi yanzu ba tare da bayyana gaskiya ba.
Majalisar ta bayyana cewa an karkatar da labarin ne domin yaudara da kuma rikita al’umma, tana mai jaddada cewa Sarkin Musulmi ba ya shiga harkokin siyasa.
Ta kuma ce matsayin Sarkin Musulmi a lokacin da kuma yanzu bai sauya ba, inda yake ci gaba da yin kira ga matakan da za su rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.
Majalisar ta kara da cewa babu wata zanga-zanga ko tashin hankali da ke gudana a fadar ko kewayenta, inda ta ce ana ci gaba da samun cikakken zaman lafiya.
A karshe, kakakin majalisar, Aminu Haliru Gidadawa, ya bukaci jama’a su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin yadawa, yana mai gargadin cewa yada tsoffin hotuna ko bidiyo na iya rikita al’umma.
