Gwamnatin Amurka ta taya ’yan Nijeriya murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da sake jaddada ƙudirin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Jaridar Punch ta ruwaito ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin mai magana da yawunta ya fitar ranar Alhamis.
Inda ta kuma ce tana daraja alaƙarta da Nijeriya tare da yaba wa ƙasashen biyu kan tattaunawar da suka gudanar cikin shekarar da ta gabata.
Amurka ta bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ke da girman dimokuraɗiyya a Afirka kuma cikin manyan ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki na nahiyar.
Hakazalika ta jaddada cewa Nijeriya na da muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin.
Gwamnatin Amurkan ta ce ƙasashen biyu na da muradu iri ɗaya a fannoni da suka haɗa da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya, kare ’yancin addini, bunƙasa harkokin kasuwanci da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Ta kuma bayyana fatan ganin Nijeriya ta ci gaba da samun zaman lafiya, haɗin kai da wadata, tare da yi wa ƙasar da al’ummarta fatan samun ci gaba da kyakkyawar makoma ga tsararraki masu zuwa.
