Rasuraj Chakraborty, wani mara lafiya mai fama da matsananciyar cutar hanta a India, ya rasu bayan ’yan sanda sun tsayar da motar asibitin da ke ɗauke da shi domin ba ayarin motocin babban ministan jihar Assam, Himanta Biswa Sarma, damar wucewa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai Chakraborty, mazaunin Bangar da ke gundumar Sribhumi, zuwa Silchar Medical College and Hospital ne domin samun ƙarin kulawar lafiya bayan halin da yake ciki ya tsananta.
Rahotanni sun ce ’yan sandan da ke kula da zirga-zirga sun tsayar da motar asibitin mai lamba 108 a yankin Ramnagar ISBT da ke Silchar domin ayarin babban ministan ya wuce.
An tabbatar da mutuwar Chakraborty a asibitin a ranar 1 ga Oktoba, 2026, lamarin da ya jawo cece-kuce da fushin jama’a a jihar Assam bayan hotunan abin da ya faru sun bazu a kafafen sada zumunta.
Hukumomi sun dakatar da jami’an ’yan sanda huɗu da ake danganta su da lamarin. Sai dai Sarma ya ce a ranar Alhamis cewa mutuwar mara lafiyar ba ta da alaƙa da ɗan lokacin da aka dakatar da motar asibitin domin ayarinsa ya wuce.
Sarma ya nemi afuwar jama’a, yana mai cewa bai kamata a hana motocin asibiti, motocin kashe gobara ko sauran ayyukan gaggawa wucewa saboda ayarin jami’an gwamnati ba. Ya kuma ce bai kamata zirga-zirgar ayarinsa ko na wani minista ta jefa jama’a cikin wahala ba.
Ofishin babban ministan ya kuma umarci kwamishinonin gundumomi da manyan jami’an ’yan sanda da su tabbatar da cewa ba a sake hana motocin da ke bukatar gaggawa wucewa saboda ayarin motocin manyan jami’an gwamnati ba.
