DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 2, 2026
HomeSiyasaTalauci da rashin tsaro sun hana 'yan Nijeriya murnar samun 'yancin kai...

Talauci da rashin tsaro sun hana ‘yan Nijeriya murnar samun ‘yancin kai – Sowore

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce ’yan Nijeriya ba za su iya yin cikakken bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai ba, matuƙar miliyoyin jama’a na ci gaba da fuskantar talauci, yunwa, rashin aikin yi da rashin tsaro.

Jaridar Punch ta ruwaito Sowore ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Ya ce duk da samun ’yancin kai, har yanzu miliyoyin ’yan Nijeriya ba su samu wasu muhimman abubuwan da ’yancin kai ya kamata ya samar ba, kamar walwala, mutunci, adalci, daidaito da ci gaban tattalin arziki.

Sowore ya kuma soki halin da ilimi, kiwon lafiya da wutar lantarki ke ciki, tare da zargin wasu daga cikin waɗanda aka damƙa musu dukiyar ƙasa da yin almundahana da dukiyar jama’a.

Ya ce matsalar Nijeriya ba ’yan ƙasar ba ce, yana mai bayyana su a matsayin mutane masu ƙwazo, basira da juriya. Sai dai ya zargi gwamnatocin da suka gabata da kasa yin amfani yadda ya kamata da dimbin albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da Nijeriya ke da su.

Dan siyasar ya ce abin da ’yan Nijeriya ke buƙata ya wuce bukukuwan cika shekara da alkawuran siyasa, inda ya ce ya kamata a samar da ƙasa da ma’aikata za su samu albashi mai ɗaukar nauyin rayuwarsu da ta iyalansu, tare da samun ingantaccen ilimi, kiwon lafiya da wutar lantarki.

Sowore ya ce babban nauyin da ke gaban wannan gwamnati shi ne sake gina Nijeriya ta yadda za ta samu ’yancin kai na gaskiya daga cin hanci da rashawa, danniya, talauci, rashin adalci, wariyar ƙabila da tsattsauran ra’ayin addini.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata