Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta sanar da kammala jigilar dawo da dukkan alhazan Nijeriya daga Ƙasar Saudiyya bayan gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jirgi na ƙarshe da ke ɗauke da alhazan Jihar Zamfara ne ake sa ran zai isa Najeriya a yau, 23 ga Yuni, 2026, wanda hakan ke nuna ƙarshen aikin jigilar alhazai na bana gaba ɗaya.
Hukumar ta ce kammala jigilar dawowar alhazai ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan ayyukan ƙasa da aka gudanar cikin nasara, wanda ya haɗa da jigilar dubban alhazan Nijeriya zuwa da kuma dawowarsu daga ƙasa mai tsarki.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa har yanzu akwai alhazan Najeriya 12 da ke ci gaba da karɓar magani a asibitoci daban-daban da ke Saudiyya sakamakon matsalolin lafiya. NAHCON ta tabbatar da cewa tana sa ido sosai kan halin da suke ciki tare da shirya yadda za a dawo da su gida cikin aminci da zarar likitoci sun sallame su daga asibiti.
Shugaban NAHCON, Ambassador Ismail Abba Yusuf, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da aka samu wajen gudanar da Hajjin 2026.
Hukumar ta kuma nuna godiyarta ga Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin da sukai jigilar Hajji masu lasisi, abokan hulɗar jiragen sama, ƙungiyoyin likitoci, jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai da kuma alhazan Najeriya saboda haɗin kai da jajircewar da suka nuna yayin gudanar da aikin.
NAHCON ta amince cewa kamar yadda ake samu a manyan ayyuka irin wannan, an fuskanci wasu ƙalubale a yayin gudanar da Hajjin bana. Sai dai ta ce an koyi darussa masu muhimmanci daga waɗannan ƙalubalen, kuma za a yi amfani da su wajen inganta ayyukan Hajji na gaba.
A wani ci gaba kuma, hukumar ta sanar da fara shirye-shiryen Hajjin shekarar 1448H/2027 tun daga yanzu domin tabbatar da kyakkyawan tsari da ingantaccen aiki. Ta ce an sanar da dukkan masu kula da harkokin Hajji a Najeriya hakan ne ta hanyar wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Yuni, 2026 mai taken “Commencement of Preparations for 1448H/2027 Hajj Season.”
Takardar, wadda Sakataren Hukumar, Dr. Mustapha Muhammad Ali, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Hukumar, ta umarci Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kuma kamfanonin yawon Hajji masu lasisi da su fara dukkan shirye-shiryen da suka dace cikin gaggawa.
Hukumar ta jaddada cewa dukkan masu ruwa da tsaki za su bi ƙa’idoji da tsare-tsaren da hukumar aikin Hajj da Umrah ta Saudiyya ta gindaya domin gudanar da Hajjin shekarar 2027 cikin nasara da inganci.
