Jam’iyyar APC ta nada Ministan Babban Birnin tarayyar Nijeriya Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke da kuma Gwamnan Jihar Anambra Chukwuma Soludo a matsayin masu jagorantar yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a jihohinsu gabanin babban zaben 2027.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jam’iyyar ta bayyana nadin nasu a cikin sabon jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa, wanda ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai kaddamar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba.
Nadin ya dauki hankali saboda ‘yan siyasar ukun ba sa cikin jam’iyya daya.
Wike dan jam’iyyar PDP ne, Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun a watan Agustan 2026 karkashin jam’iyyar Accord, yayin da Soludo ya samu wa’adin mulki na biyu a watan Nuwamban 2025 karkashin jam’iyyar APGA.
A tsarin da aka fitar, Wike zai jagoranci ayyukan yakin neman zaben APC a jihar Rivers da babban birnin tarayya, Soludo zai kula da ayyukan yakin neman zaben a Anambra, shi kuma Adeleke ya jagoranci na Jihar Osun.
Haka kuma, Ministan harkokin ruwa da tattalin arzikin rzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ya samu mukamin mataimakin babban mai kula da hada kan masu ruwa da tsaki na ɗaya a yankin kudu maso Yamma.
Shugaba Tinubu, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na APC, zai jagoranci kwamitin a matsayin shugabansa, yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, zai zama mataimakinsa.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Nentawe Yilwatda, shi ma an nada shi mataimakin shugaban kwamitin.
Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodimma, zai zama sakataren kwamitin, yayin da Surajudeen Basiru zai zama mataimakin sakatare, Hadiza Usman kuma mataimakiyar sakatare ta biyu.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen da Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq su ne mataimakan shugabannin kwamitin na daya, na biyu da na uku.
Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni zai zama mataimakin darakta-janar na farko mai kula da yankin Arewa, yayin da mataimakin Shugaban Majalisar dattawa, Barau Jibrin zai zama mataimakin darakta-janar na biyu a yankin.
Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa Adams Oshiomhole kuma zai kula da harkokin hada kan magoya baya.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele da mataimakin kakakin Majalisar makilai Benjamin Kalu, aka nada mataimakan darakta-janar na farko da na biyu masu kula da yankin Kudu.
Gwamnonin APC sun zama masu jagorantar yakin neman zabe a jihohinsu.
Wani muhimmin bangare na sabon jerin sunayen shi ne nada dukkan gwamnonin APC guda 32 a matsayin masu kula da yakin neman zaben shugaban kasa a jihohinsu.
Sai dai jam’iyyar ta kuma nada ‘yan takararta a jihohin da ba ta da gwamna domin su jagoranci ayyukan yakin neman zaben a wuraren.
Dan takarar gwamnan APC a Oyo, Sharafadeen Alli shi zai jagoranci yakin neman zaben jam’iyyar a jihar.
Mohammed Abubakar, dan takarar gwamna a Bauchi zai kula da yakin neman zaben a jihar, yayin da Chijioke Chukwu zai jagoranci na Abia.
Bugu da kari, jam’iyyar ta nada masu ba da shawara guda 14 ga kwamitin, cikinsu akwai tsohon gwamnan Osun Bisi Akande, tsohon gwamnan Ogun Segun Osoba, Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume, tsohuwar Sanata mai wakiltar Cross River ta kudu Florence Ita-Giwa, tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun da tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa, Iyiola Omisore.
An kuma sanya sunan tsohon Ministan tattalin arziki mai kula da ayyukan hadin gwiwa, Wale Edun cikin masu ba da shawara.
Ana sa ran kwamitin zai tsara tare da jagorantar ayyukan yakin neman zaben APC gabanin babban zaben 2027, ciki har da hada kan magoya baya, tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma kokarin samun goyon bayan jama’a domin sake zaben Shugaba Tinubu.
