Wasu tsoffin sojojin Nijeriya sun tare ƙofar ofishin hukumar kula da Fansho ta sojoji da ke Dutse Alhaji a Abuja.
Sun yi hakan ne domin nuna rashin amincewarsu da tsarin da hukumar ta bi wajen ƙara musu kuɗin fansho.
Tsoffin sojojin sun yi amfani da tantuna da kujeru wajen tare ƙofar ofishin, yayin da sojoji ɗauke da makamai suka hana su shiga harabar wurin.
Wannan mataki ya zo ne makonni bayan da tsoffin sojojin suka gudanar da zanga-zanga a ma’aikatar tsaro a watan Satumba, inda suka buƙaci a ƙara musu fansho sakamakon ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke bakin aiki.
Ministan Tsaro Christopher Musa, ya yi musu alƙawarin cewa za su fara samun ƙarin kuɗin fansho a watan Oktoba.
A wata hira da wakilin jaridar Punch ya yi da shi a ranar Litinin, mai tsara ayyukan ƙungiyar tsoffin sojojin Nijeriya, laftanar kanal Innocent Azubike ya zargi hukumar fanshon da amfani da tsarin ƙarin fansho da ya tauye haƙƙin wasu daga cikin waɗanda suka yi ritaya.
Azubike ya ce an shirya zanga-zangar ne sakamakon ƙara samun rashin gamsuwa tsakanin tsoffin sojojin kan yadda ake aiwatar da ƙarin fanshon da ya kamata ya biyo bayan ƙarin albashin sojojin da ke aiki.
Ya bayyana cewa babban abin da ke damun tsoffin sojojin shi ne tsarin lissafin ƙarin fanshon, wanda suke ganin bai yi la’akari da ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke bakin aiki yadda ya kamata ba.
Wannan sabon mataki ya nuna alamar har yanzu akwai saɓani tsakanin tsoffin sojojin da hukumomin da abin ya shafa kan yadda za a aiwatar da alƙawarin ƙara musu kuɗin fansho.
