DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaAPC ta tsawaita wa’adin sayar da fom ga masu neman takara

APC ta tsawaita wa’adin sayar da fom ga masu neman takara

Jam’iyyar APC ta sanar da tsawaita wa’adin sayar da fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara, tare da yin gyara a jadawalin tantance ’yan takara gabanin zaɓen shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin ta ce a sabon jadawalin, an tsawaita sayar da fom ɗin takara har zuwa tsakar dare na ranar 6 ga Mayu, 2026, yayin da aka ɗaga ranar ƙarshe ta miƙa fom ɗin da aka cika zuwa tsakar dare na ranar 7 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da tantance ’yan takara daga ranar 8 zuwa 12 ga Mayu, 2026, yayin da za a fitar da jerin sunayen waɗanda suka samu nasarar tsallake tantancewa a ranar 13 ga Mayu, 2026.

APC ta jaddada kuɗaɗen fom ɗin takara a matakai daban-daban, inda ta ce fom ɗin takarar shugaban ƙasa yana nan a kan Naira miliyan 100.

Haka kuma, masu neman takarar gwamna za su biya Naira miliyan 50, yayin da ’yan takarar majalisar jiha za su biya Naira miliyan 6.

Ga masu neman kujerar majalisar wakilai kuwa, za su biya Naira miliyan 10, yayin da masu neman kujerar majalisar dattawa za su biya Naira miliyan 20.

Jam’iyyar ta bayyana cewa tun farko ta fara sayar da fom ɗin takarar ne tun ranar Talata da ta gabata domin masu sha’awar tsayawa takara a zaɓen 2027.

Sai dai jadawalin farko ya nuna cewa za a fara sayar da fom ɗin daga ranar 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026, amma an samu jinkiri na kwanaki uku kafin a fara, wanda ya sa aka ɗauki matakin tsawaita wa’adin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata