Jam’iyyar Labour Party ta sanar da fara sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan kuɗi har Naira miliyan 50, tare da fitar da jadawalin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani na shekarar 2026 gabanin babban zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jam’iyyar ta fitar da jadawalin ne ta bakin Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ken Eluma Asogwa.
Sanarwar ta nuna cewa za a fara sayar da fom ɗin takara daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu, yayin da za a karɓi fom ɗin da aka cika daga ranar 17 zuwa 18 ga Mayu, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen fidda gwani.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa za a tantance ’yan takarar majalisar jiha da gwamna a ranar 20 ga Mayu, yayin da na majalisar ƙasa da shugaban ƙasa za su gudana a ranar 22 ga Mayu, sannan a fitar da sakamakon tantancewar a ranar 23 ga Mayu.
Kazalika, an tanadi ranakun karɓar ƙorafe-ƙorafe da daukaka ƙara a ranakun 24 da 25 ga Mayu, kafin a fitar da jerin sunayen ’yan takarar da aka amince da su a ranar 26 ga Mayu.
Jam’iyyar ta bayyana cewa za a gudanar da na zaɓen fidda gwani na majalisar jiha da gwamna a ranar 27 ga Mayu, yayin da na majalisar ƙasa da shugaban ƙasa za su gudana a ranar 29 ga Mayu.
Jam’iyyar ta ce ’yan takarar majalisar jiha za su biya Naira miliyan 3, na majalisar wakilai Naira miliyan 5, na majalisar dattawa Naira miliyan 10, yayin da na gwamna zai kai Naira miliyan 25.
An sanya Naira miliyan 10 a matsayin kudin fom ɗin nuna sha’awa da kuma Naira miliyan 40 a matsayin fom ɗin tsayawa takara, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 50.
Sai dai jam’iyyar ta yi sassauci ga mata, matasa masu shekaru tsakanin 25 zuwa 30, da kuma masu nakasa, inda ta ce su za su biya kuɗin fom ɗin nuna sha’awa kawai a dukkan matakan takara.
Bugu da ƙari, jam’iyyar ta sanar da cewa za ta bai wa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, fom ɗin takarar gwamna kyauta, a matsayin wani ɓangare na goyon bayan jam’iyyar gare shi.
