Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki alkiblar tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ma’aikatan Nijeriya ne ke ɗaukar mafi yawan nauyin wahalhalun da manufofin suka janyo.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, Atiku ya ce bikin Ranar Ma’aikata ta 2026 bai zo da murna ba, sai dai ya zama lokaci na tunani kan halin da ma’aikata ke ciki.
Ya ce, “Ranar Ma’aikata ta wannan shekara ba lokaci ne na farin ciki ba ga miliyoyin ‘yan Nijeriya, sai dai tunatarwa ce kan alkawuran da ba ao cika ba da kuma nauyin da aka ɗora wa ma’aikata.”
Ya soki cire tallafin man fetur, yana mai cewa duk da cewa dole ne a yi hakan, amma an aiwatar da shi cikin gaggawa ba tare da tsari da kariya ga talakawa ba.
A cewarsa, hakan ya jawo tashin gwauron zabi a farashin sufuri, abinci da sauran kayayyakin masarufi, ba tare da karin albashi ko tallafi mai ma’ana ga ma’aikata ba.
Atiku ya kuma nuna damuwa kan yadda aka sarrafa kuɗaɗen da aka ce an ajiye daga cire tallafin, yana mai cewa yawancin ‘yan Nijeriya ba su ga wani sauyi a rayuwarsu ba.
Ya bukaci gwamnati ta fito da manufofi da za su rage wa ma’aikata nauyi, ciki har da karin albashi, tallafi na musamman da kuma saka jari a fannin lafiya da ilimi.
Ya ƙara da cewa, “Ci gaban tattalin arziki dole ne ya mayar da hankali kan jama’a. Duk wani ci gaba da bai inganta rayuwar ma’aikata ba, ba mai dorewa ba ne.”
A ƙarshe, Atiku ya bayyana goyon bayansa ga ma’aikatan Nijeriya, yana mai kira ga gwamnati ta saurari koken su tare da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
