DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeKetareAmurka za ta janye sojojinta 5,000 daga Jamus

Amurka za ta janye sojojinta 5,000 daga Jamus

Ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa Sakataren Tsaro, Pete Hegseth, ya bayar da umarnin janye kusan sojoji 5,000 daga Jamus cikin watanni shida zuwa goma sha biyu masu zuwa.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sabani tsakanin Amurka da ƙasashen Turai kan yakin Gabas ta Tsakiya, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma sanar da karin harajin shigo da motoci daga Tarayyar Turai zuwa kashi 25 cikin 100.

Kakakin Pentagon, Sean Parnell, ya ce an yanke shawarar ne bayan nazari kan yadda ake tsara sojojin Amurka a Turai da kuma yanayin tsaro a yankin.

A cewar Trump, ya dade yana sukar ƙasashen Turai kan rashin ɗaukar nauyin tsaronsu, yana mai cewa dole ne su rage dogaro da Amurka.

Rahotanni sun ce a yanzu akwai sama da sojojin Amurka 36,000 a Jamus, yayin da Italiya ke da sama da 12,000, Spain kuma kusan 3,800.

A gefe guda, Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul, ya ce ƙasarsa na shirin karɓar wannan sauyi, amma ya jaddada cewa manyan sansanonin Amurka kamar Ramstein Air Base na da muhimmanci sosai.

Tarayyar Turai ta ce kasancewar sojojin Amurka a nahiyar yana da amfani ga bangarorin biyu, yayin da ake ci gaba da damuwa kan tsaro tun bayan mamayar Ukraine da Rasha ta yi a 2022.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata