DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaBabachir Lawal ya dora alhakin korarsa daga mukamin SGF a wuyan Osinbajo

Babachir Lawal ya dora alhakin korarsa daga mukamin SGF a wuyan Osinbajo

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya mayar da martani kan cece-kucen da suka biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADC.

A kwanakin baya, Lawal ya sanar da ficewarsa daga ADC, yana mai zargin jam’iyyar da watsi da tsarin dimokuradiyya a cikin gida. Ya ce an karkatar da zaben fidda gwani na shugaban kasa da sauran mukamai domin fifita Atiku Abubakar da magoya bayansa.

A cewarsa, an ware wasu halastattun ‘yan takara daga fafatawar, yayin da aka riga aka tsara sakamakon wasu zabukan tun kafin a gudanar da su. Ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama a jam’iyyar da ya ke ganin an mayar da ita wata kafa ta tabbatar da takarar Atiku a zaben shugaban kasa na 2027 ba.

Sai dai sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta sun jawo suka daga wasu magoya bayan Atiku. Duk da haka, Lawal ya ce bai damu da wadannan suka ba, yana mai jaddada matsayinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lawal ya ce ikirarin cewa an kore shi daga mukaminsa saboda laifin rashawa ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, Buhari ya kasance mai ba shi shawara tun daga shekarar 1971, kuma shi ne ya gayyace shi cikin tawagarsa tun a shekarar 2002. Ya ce wasu mutane sun fara jin tsoron cewa Buhari na shirin ba shi wani babban matsayi a gaba, lamarin da ya sa suka nemi hanyar cire shi daga mukami.

Ya kuma yi ikirarin cewa wasu sun yi adawa da nadinsa saboda ya fito daga kabilar Kilba kuma Kirista ne.

Ya ce duk da matsin lambar da aka yi wa Buhari, shugaban bai amince da bukatar cire shi ba.

Ko da yake bai ambaci suna kai tsaye ba a farkon bayaninsa, daga baya Lawal ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da taka muhimmiyar rawa wajen korarsa.

Ya ce bayan Majalisar Dattawa ta gabatar wa Buhari rahoton wucin gadi tana neman a kore shi, shugaban ya yi watsi da rahoton bisa shawarar Ministan Shari’a, wanda ya ce babu cikakkiyar hujja a cikinsa.

Sai dai Lawal ya ce Osinbajo ya ci gaba da matsa wa Buhari lamba kan batun har sai shugaban ya amince da kafa kwamitin bincike.

Inda a karshe ya ce rahoton wannan binciken ne ya bayar da shawarar a cire shi daga mukami duk da cewa babu wata hujja da ta nuna ya aikata laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata