DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeKetareBabban hafsan sojin Uganda ya rufe manyan kafafen yaɗa labarai masu zaman...

Babban hafsan sojin Uganda ya rufe manyan kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu

Babban Hafsan Sojin Uganda, Janar Muhoozi Kainerugaba, ya bayar da umarnin rufe wasu manyan kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu a ƙasar, yana mai cewa bai yarda da cikakken ‘yancin aikin jarida ba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ruwaito cewa Janar Muhoozi, ɗan Shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya sanar da matakin ne ta shafinsa na X .

Janar Muhoozi ya bayyana cewa an rufe tashar NTV Uganda da kuma jaridar Daily Monitor, yana mai cewa daga yanzu kafafen yaɗa labarai a Uganda za su kasance ƙarƙashin jagorancin masu goyon bayan gwamnati.

Ya rubuta cewa, “A Uganda, ban yarda da ‘yancin aikin jarida ba, dole ne kafafen yaɗa labarai su kasance ƙarƙashin jagorancin masu juyin juya hali.”

Bayan sanarwar, jaridar Daily Monitor ta ce sojoji sun kewaye hedikwatarta da ke Kampala, inda suka hana ma’aikata shiga ko fita daga ofisoshin kamfanin.

Haka kuma rahotanni sun nuna cewa tashoshin Dembe FM, Spark TV, KFM da kuma The East African, waɗanda duk ke ƙarƙashin kamfanin Nation Media Group (NMG), sun fuskanci irin wannan mataki.

Janar Muhoozi ya kuma bayar da umarnin kama Daraktar Kamfanin NMG, Susan Nsibirwa, amma daga baya ya janye umarnin bayan mai magana da yawun gwamnatin Uganda, Alan Kasujja, ya shiga tsakani.

Janar ɗin ya zargi kamfanin Nation Media Group da yi masa suka tsawon shekaru, yana mai cewa matakin da ya ɗauka ya samu amincewar mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkin Uganda.

Kungiyar Kare ‘Yan Jarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ) ta yi Allah wadai da matakin, tana mai cewa amfani da jami’an tsaro wajen rufe kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu babbar barazana ce ga ‘yancin faɗin albarkacin baki da dimokuraɗiyya.

A nata bangaren, kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Vocal Africa ta bukaci gwamnatin Uganda ta janye sojoji daga ofisoshin NMG tare da maido da dukkan tashoshin da aka dakatar, tana mai bayyana lamarin a matsayin yunƙurin danne kafafen yaɗa labarai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata