DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiBabu bushasha a bikin samun 'yancin kan Nijeriya na bana in ji...

Babu bushasha a bikin samun ‘yancin kan Nijeriya na bana in ji Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta gudanar da bikin cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai cikin sauƙi, yayin da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ’yan ƙasa jawabi a ranar 1 ga Oktoba.

Ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya Sanata George Akume ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da jaridar Saturday PUNCH ta samu.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta ƙaddamar da wani kwamiti mai wakilai daga ma’aikatu daban-daban domin shirya bikin a Abuja, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ke jagoranta.

Da yake magana bayan ƙaddamar da kwamitin, Akume, wanda Babban Sakataren Ofishin Harkokin Siyasa da Tattalin Arziƙi, Bekearedebo Warrens ya wakilta, ya ce bikin zai ba ’yan Nijeriya damar tunawa da gudunmawa da sadaukarwar waɗanda suka kafa ƙasar tare da sauran jaruman da suka yi fafutukar ganin Nijeriya ta samu ’yancin kai daga mulkin mallaka.

Ya ce nasarorin da Nijeriya ta samu tun daga shekarar 1960 sun samo asali ne daga tubalin da masu kishin ƙasa suka shimfiɗa, kuma ya ce bikin zai bai wa gwamnatin damar bayyana sauye-sauyen da ta aiwatar da kuma nasarorin da ta samu duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da zamantakewar da ƙasar ke fuskanta.

Sakataren na gwamnatin Nijeriya ya jaddada cewa za a gudanar da bikin ba tare da bushasha ba, tare da buƙatar mambobin kwamitin su gaggauta gudanar da ayyukansu saboda ƙarancin lokacin da ya rage kafin ranar 1 ga watan Oktoba.

Za a gudanar da lacca ta musamman kan ranar samun ’yancin kai a ranar 30 ga Satumba, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabin ƙasa baki ɗaya a ranar 1 ga Oktoba.

Mambobin kwamitin sun haɗa da Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙi, Taiwo Oyedele; Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris; Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo; Ministan harkokin waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu; Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Abubakar Atiku Bagudu.

Sauran mambobin sun haɗa da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; mai bai wa Shugaban sasa shawara kan daidaita manufofi, Hadiza Usman; mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan yaɗa yabarai da dabarun sadarwa Bayo Onanuga da kuma mai bai wa Shugaban Tinubu Shawara kan yaɗa labarai da sadarwar Sunday Dare.

Haka kuma, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu; Darakta-Janar na Hukumar DSS, Adeola Ajayi da Kwamandan rundunar Guards Brigade, Adebisi Onasanya na cikin kwamitin tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata