DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiBai kamata a riƙa tura sojoji aikin tsaron zaɓe a Nijeriya ba...

Bai kamata a riƙa tura sojoji aikin tsaron zaɓe a Nijeriya ba – INEC

Shugaban hukumar zaɓen Nijeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce bai kamata a riƙa tura jami’an soji domin tsaron wajen zaɓe ba, yana mai jaddada cewa hakan ya kamata ya kasance ne idan akwai matsalar tsaro ta musamman.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban INEC ya bayyana hakan ne ta bakin daraktan harkokin shari’a na hukumar, Al-Hassan Umar, yayin wani taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abuja.

Amupitan ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya fayyace cewa INEC ce ke da alhakin gudanar da zaɓe, yayin da rundunar ’yan sandan Nijeriya ita ce babbar hukuma da ke jagorantar tsaron zaɓe.

Ya bayyana cewa rawar da sojoji ke takawa a lokacin zaɓe ita ce ta tallafawa hukumomin farar hula kawai idan yanayin tsaro ya zama dole, kuma bisa tanadin kundin tsarin mulki da sauran dokoki.

A cewarsa, ayyukan da sojoji za su iya yi sun haɗa da kare muhimman wuraren gwamnati da kayayyakin more rayuwa, taimakawa wajen jigilar kayan zaɓe masu muhimmanci idan bukatar hakan ta taso, da kuma taimaka wa hukumomin tsaro wajen magance matsalolin tsaro na musamman.

Shugaban na INEC ya kuma buƙaci jami’an soji da su kasance tsaka-tsaki a harkokin siyasa idan aka tura su aikin tsaron zaɓe, yana mai cewa aikin su shi ne kare kundin tsarin mulki da ƙasar Nijeriya, ba wata jam’iyya ko ɗan takara ba.

Ya ƙara da cewa yayin da ake shirin babban zaɓen 2027, barazanar tsaro ba ta tsaya kan tashin hankali kawai ba, har ma ta haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane, yaɗa bayanan ƙarya da kuma amfani da fasahar zamani wajen katsalandan a harkokin zaɓe.

Amupitan ya tabbatar da cewa INEC na ci gaba da aiki tare da kwamitin haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa mai cancanta zai iya kaɗa ƙuri’arsa cikin ‘yanci, aminci da ba tare da tsoratarwa ba.

Shi ma da yake jawabi, wakilin babban hafsan tsaron Nijeriya, Rear Admiral Abolade Ogunleye, ya ce rundunar sojin ƙasar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da mutunta haƙƙin ɗan Adam idan aka buƙaci taimakonta wajen tsaron zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata