Hukumar kula da basussuka ta Nijeriya, DMO, ta bayyana cewa jimillar bashin da ƙasar ta ciwo ya karu zuwa Naira tiriliyan 159.28 ya zuwa ƙarshen Disambar, 2025, lamarin da ke nuna ƙaruwar bashi a tattalin arziƙin ƙasar.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa rahoton da DMO ta fitar, ya nuna cewa bashin ya tashi daga Naira tiriliya 153.29 a watan Satumba 2025 zuwa Naira tiriliyan 159.28 a watan Disamba, wanda ke nuna ƙaruwar bashin da kashi 3.9%).
Haka kuma idan aka kwatanta da shekarar 2024, bashin ya karu da Naira tiriliyan 14.6 , daga tiriliyan 144.67.
A cewar rahoton, bashin cikin gida shi ne wanda yafi yawa, inda ya kai Naira tiriliyan 84.85, wanda ya kai kashi 53.27% na kafatanin bashin da ake bin ƙasar.
Bashin da ƙasar ta ciwo a ƙasashen waje yanzu ya kai Naira tiriliyan 74.43, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 46.73%, wanda hakan ya nuna cewa Nijeriya na ci gaba da dogaro da bashin cikin gida wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
