Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Honarabul Mohammed Bello El-Rufai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa ADC tare da bayyana cewa zai sake neman zaɓe a ƙarƙashin sabuwar jam’iyyar.
Mohammed Bello El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa bayan kakakin majalisar wakilai, Honarabul Tajudeen Abbas, ya karanta takardar ficewarsa daga APC a zaman majalisa.
DCL Hausa ta ruwaito cewa ɗan majalisar ya ce Honarabul Suleiman Richifa mai wakiltar Soba da Honarabul Umar Ajilo mai wakiltar Makarfi/Kudan su ma sun koma ADC domin gina jam’iyyar da za ta mayar da hankali kan hidimtawa jama’a.
Ya ce matakin da ya ɗauka ba mai sauƙi ba ne, yana mai cewa a matsayinsa na ɗan tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai, yana aik ne bisa jajircewa da kishin samar wa jama’a kyakkyawan wakilci.
Mohammed Bello El-Rufai ya tabbatar wa al’ummar Kaduna ta Arewa cewa aikinsa zai ci gaba ba tare da tangarda ba, yana mai cewa akwai sauran ayyuka masu yawa da zai aiwatar.
Ya kuma bayyana cewa nan gaba kaɗan zai sanar da kwamitin wucin gadi na shirin kula da cibiyoyin lafiya na matakin farko da ya ƙaddamar a makon da ya gabata.
A cewarsa, za a fara rabon kayan lafiya ciki har da allurai 1,000 ga kowace cibiyar lafiya a mataki na farko, wanda zai fara da cibiyoyin Unguwar Sarki da Badarawa/Malali.
