Majalisun dokokin ƙasar Birtaniya sun amince da wata doka da za ta hana sayar da sigari ga duk wanda aka haifa bayan shekarar 2008, a wani mataki na rage shan taba a nan gaba.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, dokar mai suna Tobacco and Vapes Bill na nufin hana duk wanda aka haifa bayan 1 ga Janairu 2009 sayen sigari har tsawon rayuwarsa.
Ministan Lafiya, Wes Streeting, ya bayyana wannan mataki a matsayin “muhimmi ga lafiyar ƙasa,” yana mai cewa zai taimaka wajen samar da ƙarni na farko da ba su shan taba.
Dokar za ta kuma bai wa gwamnati damar faɗaɗa dokar hana shan taba zuwa wasu wurare na waje kamar filayen wasa na yara da kusa da makarantu da asibitoci, tare da sanya takunkumi kan ɗanɗanon sigari ta zamani da yadda ake shirya su.
Haka kuma, an ce matakin na cikin shirin rage matsin lamba ga tsarin kiwon lafiya na ƙasar (NHS), yayin da rahotanni ke nuna cewa shan taba na haddasa mutuwar kusan mutum 75,000 a duk shekara a Ingila.
